SHIAH: NASIHA DAGA BAKIN MAI MARTABA SARKIN KANO MUHAMMADU SUNUSI NA BIYU.

 

via: Yasir Ramadan Gwale​

17-12-2015

A dangane da abinda ya faru a Zaria, Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu yayi Nasiha mai ratsa zukata akan wannan batu. Ya kuma yi kira mai matukar muhimmanci. Na san da yawan mutanan Kano sun saurara jiya a Freedom Radio.

Tun lokacin da akai wannan batarna’ka tsakanin yaran Sayyid Zakzaky da Sojoji na zabi kame baki na kan wannan lamari, domin abu ne da nake gani tsakanin sojoji da masu kunnen k’ashi. Cikin ikon Allah, daya daga cikin abinda yake damuna a Rai sosai game da Shiah da Zakzaky, mai martaba Sarkin Kano ya wanke mun shi.

Ta bakin Sarkin Kano, Kasar Najeriya an gina Musulunci ne a bisa doron Ahlussunnah Wal Jama’ah. Dan haka duk wanda ya zo da batun darikun sufaye da sauran su, to daga baya ya zo da shi. Haka kuma, kamar yadda Sarkin ya fada, tun farko anyi sakaci, domin, an san Da’awar Zakzaky karya ce ba Musulunci bane, akai shiru aka barshi ya shiga kauyuka ya tara jahilai a matsayin mabiya, har yake neman zamarwa al’umma barazana shi da mabiyansa na kin mutunta dan Adam da kuma dokokinsa hukuma.

Tabbas akwai laifin Sarakuna wajen yaduwar Shiah a Najeriya, domin sun san tushen Musulunci babu aqidar Zagin sahabbai ko Matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, amma sabida ana ganin Ahlussunnah ne ke adawa da abin da kuma kausasa harshe akan koyarwar Shiah, sai ake ganin kamar matsala ce da ta shafi Ahlusunnah ko ‘yan Izala Sarakuna sukai kurum Zakzaky na halaka musu al’umma, alhali an san karya yake yi ba Musulunci yake ba.

Alhamdulillah, ya zuwa yanzu Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya farga, kuma ya ankarar da ‘yan uwansa Sarakuna da Sauran al’umma cewar, Musulunci a Najeriya an gina shi ne akan koyarwar Ahlussunnah Wal Jama’ah, dan haka an gina mu akan mutunta dangi da iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam da suka hada da Ahlulbaity da Sahabbai da Matansa Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Allah ya sakawa Mai Martaba sarki da wannan nasiha mai matukar muhimmanci.

Kuma wani abin Albishir ga al’ummar Musulmi a Najeriya, shi ne,

Wannan Waki’a ta Zaria da ta auku tsakanin Soji da Yaran Zakzaky, tayi Sanadiyar Kawo karshen yadawar Shiah a Najeriya In sha Allah. Domin filin Husainiya da ake yin kafurci da zagin Sahabbai a cikinsa, asalin sa filin Deport ne na NA wato Chidit Barrack, shi ne Sardauna Sokoto Firimiyan Jihar Arewa Sir Ahamadu Bello ya nemi Turawa su bashi filin dan yana gina filin Polo, kuma a yarjejeniyar da akai da Soji wannan fili ba na sayarwa bane, amma aka samu wata Gwamnati a Kaduna ta maida filin Mallakarta kuma ta baiwa Zakzaky.
To Alhamdulillah yanzu haka Buratai ya ce filin Husainiya ya dawo gayaunar sojoji.

Bayan haka kuma, gidan Zakzaky da ke Gyallesu asalinsa shima Gwamnatin Abdussalam Abubakar ce ta gina masa, ta bashi kyauta a matsayin Diyyar abinda Marigayi Gen. Sani Abacha yayi masa, to al’umma dake zaune a Gyallesu sun rubuta dubban sakonnin koke koke akan irin cuzguna musu da Zakzaky da yaransa suke yi, dan haka shima wannan gida Zakzaky ya karya dokar bashi gidan, dan haka sojoji sun kwace shi.

A yanzu dai zamu iya cewa Buratai yayi Jana’izar Shiah a duk fadin Najeriya.

Saura da me?

Ya kamata al’umma su sani, kuma su fadaka, babu wata akida ta zagin Sahabbai da Iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam a cikin addinin Musulunci.

Dan haka kamar yadda mai martaba Sarkin Kano yayi kira dole Sarakuna su tashi tsaye wajen Yaki da duk wanda ya zo dan gurbata addinin Musulunci da aka gina shi akan koyarwar Ahlussunnah Wal Jama’ah a wannan kasa tamu mai Albarka.

Ya Allah kasa wannan shi ne karshen Shiah a Nijeriya. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmi ka kaskantar da Shiah da duk masu goya musu baya na saurari da na b’oye munafukai masu takiyya.

SHIN AZUMIN WATAN RAJAB (AZUMIN TSOFAFFI) YA INGANTA A SUNNAH???!!!!

SHIN AZUMIN WATAN RAJAB (AZUMIN TSOFAFFI) YA INGANTA A SUNNAH???!!!!

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam da Alayensa da Sahabbansa gaba daya da wadanda suka biyo bayan su da kyautatawa.
Wannan rubutu ya bi yo bayan wata tambaya da aka mun, akan shin ya halatta yin azumin watan Rajab?!

Wannan yasa na kudurci niyyar yin bayani akan wannan qadiyar, tare da neman taimakon Allah (SWA) da ya aka za mun ya yin wannan binciken da kuma rubutun.

WATAN RAJAB:- Yana daya daga cikin watannin musulunci guda hudu da ake kiran su da watanni masu alfarma (ASH-HURUL HURUM).
Allah (SWA) yak e cewa:-
“LALLAI QIDAYAYYUN WATANNI A WURIN ALLAH (SWA), WATA GOMA SHA BIYU NE A CIKIN LITTAFIN ALLAH, RANAR DA YA HALICCI SAMMAI DA KASSAI, A CIKIN SU AKWAI (WATANNI) HUDU MASU ALFARMA…” Suratul Taubah 36.

Watanni ma su alfarma su ne:-
RAJAB, ZUL QADAH, ZUL HIJJAH DA MUHARRAM.

Imamul Bukhari (4662) da Imam Muslim (1679) sun ruwaito hadisi daga Abi Bakharata (RA), Manzon Allah (SAW) y ace;
“A SHEKARA WATA GOMA SHA BIYU NE, A CIKIN SU AKWAI WATANNI HUDU MASU ALFARMA, UKU DAGA CIKI SUNA JERE; ZULQADAH, ZULHIJJAH DA MUHARRAM, RAJAB KUMA SHINE WANDA YA KE TSAKANIN JUMADA SANI (Watan 6) DA SHA’ABAN (watan 8).

@ An sanya musu watanni ma su alfarma ne saboda dalilai guda biyu;

(1). Haramta yin yaki a cikin su da aka yi, sai dai idan abokanan gaba ne suka fara.
(2). Ai kata mummunan aiki a cikin su, ya fi tsanani sama da sauran watannin.

Da wannan ne Allah (SWA) ya hana aikata sabo a cikin wadannan watannin.
Allah (SWA) y ace: “KA DA KU ZALUNCI KAN KU A CIKIN (wadannan) WATANNIN” Tuaba 36.
Duba Tafsirin Shaikh Nasirus Sa’adi karkashin wannan ayar shafi na (373).

AZUMI A WATAN RAJAB DA MAGANGANUN MALAMAI:-

Babu wani dalili ingatacce day a zo akan yin azumin a watan Rajab, ko hadisi ingatacce dangane da falalar azumi a watan, dukkan hadisan da suka zo hadisai ne na karya da’ifai.

Abu Dauda ya ruwaito hadisi a sunan na shi (2428) dangane da muhimmancin azumi a watanni masu alfarma. Manzon Allah (SAW) y ace: “KA AZUMCI WATANNI MASU ALFARMA…..”
Imam Albani ya Da’ifantar da hadisin a cikin Da’if Abi Dauda.

@ Shaikhul Islam Ibn taimiyyah (RH) y ace: “Ke banta watan rajab da yin azumi, dukkan hadisan da su ka zo akan haka da’ifai ne (masu rauni), bal ma hadisan karya ne, ma’abota ilimi bas a daukan hadisan a bakin komai, domin bas a cikin hadisan da ake amfani das u don nuna falalar aikata abu (Fadha’ilul A’amal), bal dukkan su ma hadisai ne na karya..”
Duba Majmu’u Fatawa (25/290).

@ Imam Ibnul Qaiyim (RH) y ace; “Dukkan hadisin day a ambaci azumin watan rajab da sallatar wasu darare a cikin sa, karya ne kirkirarre”.
Duba Almanarul Muniif (shafi 96).

@ Alhafiz Ibn Hajar Al-Asqalani yak e cewa; “Babu wani abu da aka ruwaito na falalar watan Rajab, ko yin azumi a cikin sa, ko azumtar wasu adadin kwanaki ayyanannu, ko tsayuwar wasu darare kebantattu”.
Duba Tabyinul Ajab (shafi 11).

@ Imam Sayyid Sabiq (RA) yak e cewa; “Azumin watan rajab bas hi da wani fifko na falala akan waninsa cikin watanni, sai dais hi yana daga cikin watanni (guda hudu) ma su alfarma, kuma ba a samu a cikin sunnah ingatacci cewa yin azumi a cikin sa yana da falala kebantacce, abunda ya zo akan haka (ma’ana hadisan da suka zo) ba a kafa hujja das u (domin da’ifai ne)”
Duba Fiqhus-Sunnah (1/383).

@ An tambayi Shakh Salihul Usaimeen (RH) dangane da azumi ranar 27 ga watan rajab da kuma tsayuwar dararen sa.
Sai ya amsa da cewa:
“Yin azumi ranar 27 ga watan Rajab da tsayuwar darensam kebance shi da haka bidi’a ne, dukkan bidi’a kuma bat ace”
Duba Majmu’u fatawa na Usaimeen (20/440).

A takaice da wadannan dalilai da muka ambata za mu fahimci cewa kebance watan Rajab da yin azumi ko nafilfili bai ingantaba a Sunnah.

Don haka mu tsaya a inda Sunnah ta umurce mu akai, mu guji aikata bidi’a.

Allah ya tabbatar da mu akan sunnar Manzon allah (SAW).

Wannan shine a takaice.

Dan uwanku:
Muhammad Albani Misau.
1/7/1436. 20/4/2015

RAYUWAR MUSULMI A YAU.

بسم الله الرحمن الرحيم

GABATARWA.

Wannan kalma tana iya daukan fiskoki, ko ma’anoni guda uku:-

(1) Rayuwar musulmi da ‘dan uwansa musulmi a kowani guri da kowa ce kasa.

(2) Rayuwar musulmi da wanda ba musulmi ba ta wajen zaman takewar yau da kullum.

(3) Rayuwar musulmi ga shi kansa wajen bin tsarin musulunci kamar yadda Allah ya tsara masa bisa karantarwar Manzon Allah SAW.

Wadannan fiskoki guda uku idan mukayi tadabburin ma’anonin ayoyin Alqur’ani mai girma za mu ga Allah SWA ya yi mana bayaninsu dalla dalla, daya bayan daya a cikin suratul An’ami Aya ta (151 – 153).

“قل تعالول أتل ما حرم ربكم عليكم, ألاَ تشركوا به شيئاً, وباالوالدان إحساناً ولا تقتلوا أولادكم من إملاق نحن نرزقكم و إياهم, ولا تقربوا الفواحش ماظهر منها وما بطن ولا تقتلوا النفس التى حرم الله إلا بالحق, ذالكم وصىكم به لعلكم تعقلون ” (151).
“ولا تقربوا مال اليتيم إلا بالتى هى أحسن حتى يبلغ أشده, وأوفواْ الكيل والميزان بالقسط, لا نكلف نفساً إلا وسعها, وإذا قلتم فاْعدلواْ ولو كان ذا قربى و وبعهد الله او فواْ, ذالكم وصىكم به, لعلكم تذكرون” (152).
“,أن هذا صراطى مستقيماً فاْتبعوه, ولا تتبعواْ السبل فتفرق بكم عن سبيله,ج ذالكم وصىكم به, لعلكم تتقون” (153).

Dai dai wadannan ayoyi Imam Ibn khathir cikin Tafsirinsa, ya hakaito maganan Abdullahi ‘dan mas’ud (RA) y ace

“WANDA YAKE SO YAGA WASIYYAR MANZON ALLAH (SAW) WACCE YA SANYA TAMBARINSA AKANTA, TO YA KARANTA WADANNAN AYOYI GUDA UKU”.

Sa’anan yana da kyau mu fahimci cewar bayana nufin akwai wasu ayoyi wanda Manzon Allah (SAW) ya kebe su ya musu tambari na musamman bai yu wa wassu ba, abin nufi anan shine wadannan ayoyi guda uku, hani da umaurni ko mas’aloli da Allah ya yi bayaninsu a ciki, Manzon Allah(SAW) ya karfafasu wa sahabbai akanta, kamar yadda Imamul Bagawi ya kawo cikin tafsirinsa. (Ma’alimut Tanzil, mujalladi na 2).

Sa’annan wadannan ayoyi guda uku akwai wasu mas’aloli guda goma (10) a cikin su, wadanda malamai suka musu suna da (WASAYAL ASHRA) ma’ana wasiyyoyi guda goma.

Kuma in muka fahimci kowace daya daga cikin wasiyyoyin nan guda goma (10), tana iya kasancewa cikin fiskokin rayuwar musulmi guda uku wadanda muka ambata su a baya.

Wadannan mas’aloli guda goma sune:

  • Kada kayi shirka wa Allah.

  • A kyautata wa iyaye.

  • Kada a kashe ‘ya’ya don tsoron talauci.

  • Kada a kusanci Alfasha a fili da boye.

  • Kada a kashe wata rai da Allah ya haramta sai da haqqi.

  • Kada a kusanci dukiyar maraya sai da kyautatawa.

  • A cika mudu da sikeli da adalci.

  • Abi hanyar Allah da Manzosa ba tare da yin bidi’a ba.

-In za a yi Magana a yi adalci
ko akan makusanci ne.

  • A cika Alkawarin da aka dauka wa Allah.

Wadannan sune mas’aloli guda goma wanda ayoyinnan guda uku suka kunsa, sa’annan idan muka dibi mas’aloli guda uku daga ciki:

*Kada a kashe ‘ya’ya don tsoron talauci.

  • Kada a kashe wata rai da Allah ya haramta sai da haqqi.
  • Kada a kusanci dikiyar maraya said a kyautatawa. –

Wadannan sun sha fi musulmi da ‘dan uwansa musulmi kai tsaye.

Sa’annan idan muka dubi mas’aloli guda uku daga ciki har wayau:

  • In za a ayi Magana a yi adalci ko akan makusanci ne.

*A kyautata wa iyaye.

*A cika mudu da sikeli da adalci.

Su kuma wadannan sun shafi tsakanin musulmi da wanda suke mu’amala das hi kai tsaye ko dab a musulmi ne ba.
Sa’annan sauran mas’aloli guda hudu:

  • Kada kayi shirka wa Allah-
    Kada a kusanci Alfasha a fili da boye.

-Abi hanyar Allah da Manzosa ba tare da yin bidi’a ba.
-A cika wa Allah Alqawarinsa.

Wadannan su kuma sun shafi shi musulmi ne akaran kansa.

Amma kuma wadannan mas’aloli guda goma da suka zo daga cikin wadannan ayoyi guda uku, wajibine akan dukkan musulmi ya kiyayesu kuma kada yayi sakaci das u, don hadisi ya zo daga Ubadatu dan Samit y ace Manzon Allah SAW yace: “WAYE CIKINKU ZAI YIMIN MUBAYA’A AKAN ABUUKU?” yace sai Manzon Allah SAW ya karanto wadannan ayoyi har zuwa karshensu, sai Manzon Allah ya ci gaba da cewa;

“DUK WANDA YA CIKASU TA LADANSA YANA GURIN ALLAH, DUK WANDA YA TAUYE WANI DAGA CIKINSU SAI ALLAH YA KAMASHI A DUNIYA, TO WANNAN AZABARSA, AMMA WANDA ALLAH YAJIN KIRTA MASA ZUWA LAHIRA, TO AL’AMARINSA YANA GURIN ALLAH IN YA SO YA MASA AZABA IN YA SO YA YAYEFA MASA” (duba Tafsir na Ibn Kathir, mujalladi na 2).

Imamu Hakim shi ya ruwaito wannan Hadisin a cikin littafinsa (ALMUSTADRAK), amma Imam Ibn Khathir ya hakaito shi a cikin tafsirinsa dai – dai fassarar wadannan ayoyi.

Sa’annan ina mai rokon Allah ya taimake mu wajen kiyaye hakkokin daya dora akan mu, tsakanin mu da shi da kuma na ‘yan uwan mu, musulmi da wanda ba musulmi ba, amen.

NAZARI A YAU.

‘Yan uawana musulmi kowa mai shaidane a cikinku akan halin da musulmai da musulinci ke ciki a yau, ta bangaren musulmin su kansu da kuma wadanda ma ba musulman ba, a duniya baki daya bawai a wata kasa ko a wani gari ba.

Musulmi yana cikin kaskanci da rashin mutunci da wulakanci, da zaman dar-dar, wasu alkawarin Allah ne da yayi akan wadanda suke dogewa da yin Imani na gaskiya, kamar yadda Allah SWA ya fada a cikin Alqur’ani mai girma:

“ولنبلونكم بشيء من الخوف والجوع ونقص من الأموال والأنقس والثمرات قل وبشر الصابرين” (155)
” الذين إذآ أصابتهم مصيبة قالواْ إنا لله و غنا إليه الراجيعون.(156).
” أوْلئك عليهم صلواتٌ من ربهم ورحمةصلى وألئك هم المفلحون.(157).

“WALLAHI ZAMU JARRABE KU DA WANI ABU DAGA TSORO DA YUNWA DA TAWAYA CIKIN DUKIYA DA RAYUKA DA ‘YA’YAN ITATUWA (Amfanin gona), AMMA KA YI ALBISHIR WA MASU HAKURI. SUNE IDAN WATA MUSIBA TA SHAFE SU SAI, SU CE LALLAI DAGA ALLAH MUKE KUMA GARE SHI ZA MU KOMA. WADANNAN SUNE SUKE DA SALATOTI DAGA MAHALICCINSU DA JINKAI KUMA WADANNAN SUNE SHIRYAYYU” (Baqara, Aya ta 155-157).

Kuma duk wanda ya shiga cikin tsanani saboda ya yi riko da addini to jimawa kadan zai samu sauki.

Allah SWA yana cewa
“LALLAI TARE DA TSANANI AKWAI SAUKI” (Sharhi, Aya ta 5).

Sa’annan kuma Allah zai bas hi mafita da fadinsa madaukaki

“DUK WANDA YA JI TSORON ALLAH, ALLA ZAI BA SHI MAFITA” (dalaq: 2).

To amma wadannan sune mafi kadanci a rayuwa da muke ciki a yau, don hadisi ya tabbata daga Abu Huraira (RA) yace, Manzon Allah SAW yace:

“ZAMANI YANA KUSANTOWA, AIKI ZAI YI KADAN ZA A RINKA YIN BAKAR ROWA KUMA FITINA ZA TA YI YAWA” (Bukhari 4/6652, muslim 1/157).

Da fadin Manzon Allah SWA har wa yau:

“WATA YANKI BAZATA GUSHEBA CIKIN AL’UMMATA TANA KAN GASKIYA, BA ZAI CUCESU BA, DUK WANDA YA SABA MUSU, HAR SAI AL’AMARIN ALLA Y NZO” (Muslim).

Amma mafiya yawan yawa cikinmu ba haka muke ba, mun sake tafarkin gaskiya, haramun ya zama halal, halal kuma ya zama haram, abu mummuna ammai das hi kyakkyawa, sabawa Allah ya za ma kamar da’a wa Allah, tarbiyyar musulunci ammai das hi tsohon yayi, Alqur’ani ya zama sai dai a yi takara an kaurace wa hukuncinsa, alhali babu wani alkhairi face yana cikin Alqu’ani.

Hadisi ya tabbata Manzon Allah SAW yace

“NA BAR WA SU ABUBUWA GUDA BIYU A CIKINKU, BA ZA KU TABA BACE WABA MATUKAR KUNYI RIKO DA SU, LITTAFIN ALLAH (Alqur”ani) DA SUNNATA”.

Musulmi ya sauke Alqur’ani yasa kae sunnar Manzon Allah SAW, in dai musulmi yayi haka wa kansa, mai yasa kaskanci ba zai same ba,tin da ya sake hanyar addininsa ta gaskiya.

Hadisi ya tabbata daga Abdullahi dan Umar RA yace, na ji Manzon Allah SAW yana cewa

“IDAN KU KA YI CINIKIN IINA KUKA RIKE JILAR SHA NU KUMA KU KA YARDA DA SHUKE-SHUKE, KUMA KUKA BAR JIHADI, TO ALLAH ZA SHINFIDA MUKU KASKANCI, BA ZAI CIRE SHIBA HAR SAI KUN KOMA ADDININKU” (Abu Dauda da Imam Ahmad).

Ma’anar (IINA), wani nau’I ne na saye da sayar wa, amma akwai riba a ciki, duk da cewar wasu daga cikin Malaman Fiqhu suna ganin babu laifi, amma mafi ingancin Magana wannan kasuwancin ta (IINA) bata halarta ba.(Mai neman Karin bayani ya duba Attarbiyatu wat tarbiyatu na Imam Albani).

Sa’annan wannan hadisin, kamar yadda Imamu Albani yace,” ma’anarsa idan kuka shagalta da tara kayan duniya da neman arziki, da tawilin cewa neman arzikin halalne, hart a kai mutum yana gab a abin day a zo nema duniya sai arziki kawai, to wannan shike sa mutum ya manta da Allah, kuma yayi ta saba masa”. Ya ci gaba da cewa “Wannan hadisin yana dga cikin alamomin Annabci na Manzon Allah SAW. Kamar yadda ‘yan uwa suke gani tabbas wannan kaskancin ya tabbata a cikin mu, kamar yadda Manzon Allah SAW ya fada”.
TARBIYYAR MUSULMI

Tabbas tarbiyyar musulunci iatce tarbiyya ta kololuwa, kuma babu tarbiyyar daya fishi da cewa da ‘dan Adam, kai har ma da duniya baki daya. Idan muka dubi lokacin jahiliyya mutum yakan sassake itace da hannunsa sa’annan ya mai das hi abin bautarsa, kuma gare shi yak e kai kukansa da neman agajinsa, wani kuma dutse yake dauka mai kyau ya maid a shi abin bauta.

Babu wautar daya shige irin wannan. Wani kuma sai yce duk dunuyya babu abinda ya fiso illa lokacin da dare yayi, yayi tatul da giya, yayi ta surkulle shi kadai, sa’annan ga zinace-zinace, su a gurinsu zina ba laifi ba ne, sai dai anyi a fili, amma idan an boye, babu laifi, ga fashi da makami, su a gunsu fashi da makami jarunta ne, duk wanda yafi karfi shine shugaba, sa’annan wani babban al’amari dab a komai bane a gunsu shine: kisan kai, hasalima ‘yan’yansu suke kashewa don tsoron talauci da abin kunya (wai a fadinsu), sai yake-yaken da babu gaira ba dalili, da fitan ballagaza da mata keyi, sa’annan auratayya rututu babu iyaka, su agunsu mutum zai iya auran mata sama da ‘dari ma ba laifi, sa’annan babu babba ba yaro.

Amma da Manzon Allah SAW ya kawo musu sakon Allah SWA, duk da cewa ya same su cikin lallacewa da gafala, kamar yadda Allah SWA ya fada a wata aya:

“DON KA YI GARGADI WA WASU MUTANE DA BA’A’TABA GARGADI WA IYAYENSU BA, SU SUNA CIKIN GAFALA” (Yasin Aya ta 6).

Amma duk da haka Manzon Allah (SAW) saboda iya karantarwarsa da kuma kykkyawar dabi’arsa, ya rika binsu sako-sako, wuri-wuri yana musu wa’azi da Alqur’ani, cikin yardar Allah, dabi’unsa ya canza, imaninsu ya karfafa, suka yi watsi da ‘dabi’un jahiliyya suka rike na musulunci har Allah yayi musu yabo a cikin Alqur’ani a wurare daban daban.

Kuma suka kasance cikin daukaka bayan sunyi fama da kaskanci, a lokacin jahiliyya, kamar yadda Sayyiduna Umar (RA) yake cewa:

“DA MUNA CIKIN KASKANCI, SAI ALLAH YA DAUKAKA MU DA ALQURANI, IDAN MUKA NEMI DAUKAKA BATA ALQUR’ANI BA, TO ALLAH ZAI KASKANTAR DA MU” (Duba Muqaddimatu fi Usulil tafsir).

Ma’ana: Wadancan dabi;un su suka jefa su cikin kaskanci da lalacewa, sa’annan Alqur’ani da bin tsarin musulunci shi ya fidda su daga cikin kaskanci ya sa su cikin ‘yanci da daukaka.
HALINMU A YAU.

Mu a halin da ake ciki ko a rayuwar mu ta yau, duk dabi’un jahiliyya babu daya wacce ba a yenta a yanzu ko kuma ince anzarce lokacin jahiliyyar farko, wannan kuwa shine ya afkar da mu cikin kaskancin da muke ciki a yau, Allah (SWA) yana cewa

“LALLAI ALLAH BA SHI CANZA WA MUTANE, SAI DAI SUNE SUKE CANZA WA KAWUNANSU” (Ra’adi, Ayata 11).

SHAWARWARIN GYARA.

(1). Wajibine ko wani dayan mu ya gyara alaqarsa da Mahaliccinsa Allah (SWA).

(2). Wajibine kowa ya gyara alaqarsa da jama’an da yake mu’amala das u.

(3). Wajibine kowa ya maid a hankali wajen tarbiyyar iyalansa bisa tsarin musulunci, don ya tsira a wajen Allah ranar da ‘ya’ya da dikiya ba za su amfanar das hi da komai ba, sai tsoron Allah.

(4). Wajibine kowa ya da mu da gyaruwar zuciyarsa, don samun karbuwar ayyukansa kamar yadda wani mai da’awar musulunci ke cewa

“KU TSAYAR DA DAULAR MUSULUNCI A ZUCIYARKU, SAI TA TSAYU CIKIN KASASHENKU”.

(5). Wajibine kowa ya maid a hankali wajen neman ilimin addini da rayuwa, ta yadda zai bautawa wa Allah cikin ilimi bad a jahilci ba.

Wannan shine abinda ya sauwaka daga gare ni, ina kuma rokon Allah ya ya taimake mu ya ba mu ikon aiki da abinda muka karanta, ya kuma tabbatar mana da daular musulunci a kasata Najeriya da duniya gaba daya amen.

Wa subhanakallahumma wabihamdika astagfiruka wa’atubu ilaikh.

MUHAMMAD MUHAMMAD ALBANI MISAU.

MATSALOLIN ALJANU DA YADDA ZA MAGANCE SU.

GABATARWA.

Dukkan godiya da yabo su tabbta ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da wadanda suka biyo bayan su da kyautatawa har ya zuwa ranar tashin alkiyama.

Bayan haka wannan sako ne na musamman zuwa ga ‘yan uwa musulmai maza da mata dangane da matsalolin da suka shafi matan aure da ‘yan mata musulmai da samari marasa aure da magidanta baki daya, dangane da matsalar shafar Aljanu, da yadda suke shiga jikin mutum dan Adam, da alamomin da dan Adam zai gane cewa akwai Aljanin a jikinsa, sa’annan bayani game da matsalar da ake kira (jinnul ashik) namijin dare ko (jinnu ashika) macen dare.

Allah na ke roko ya mun dace wajen wannan rubutun amen.

SU WAYE ALJANU KUMA DAGA INA ALLAH YA HALICCE SU?.

Aljanu hailttu ne da Allah (SWA) ya yahalicce ya ajiye su a duniya don su bauta masa.

Sa’annan ya halicce su ne daga harshen wuta, Allah (SWA) yana cewa :

“KUMA YA HALICCI ALJANI DAGA WUTA (Harsashen Wuta)”.

Dan Abbas y ace lallai Aljanu an halicci su daga harshen wuta.

Don haka sai muce Aljanu wasu halittu ne da Allah ya halicce su daga harshen wuta, shi yasa ba a iya ganin su, kuma ba a iya taba su ko jin mosinsu, saboda su ruhuine kawai, bas u da tabbataccen gangan jiki irin na dan Adam, shi yasa suke shiga surar irin jikin da suka ga dama, kamar Kare, Maciji, Kyanwa (Mage), da sauransu.

NAU’IN HALITTUN ALJANU.

Allah (SWA) ya halicci Aljanu da nau’in halitti mabanbanta.

An samo Hadisi daga Aba Sa’alabatal Kushaniy (RA) yace, Manzon Allah (SAW) yace: “ALJANU NAU’I UKU NE (Wasu) NAU’IN MASU FIKA FIKAINE, SUNA TASHI SAMA, DA NAU’IN MASU ZAMA MACIZAI DA KUNAMAI DA MASU ZAMA WURI DAYA SU KAURA” (Hakim ya fidda shi).

WURAREN DA ALJANU SUKE ZAMA

Sun kasance suna zama a cikin wadannan wuraren kamar haka:-

  1. Cikin Daji.

  2. Cikin Ruwa.

  3. Tsaunuka, da Koguna.

  4. . Bayan Daki

  5. Bola (Jibji).

  6. Wajen Wanke – Wanke.

  7. Wurin Makabarta.

Masu zama a cikin jama’a sun fi cutar da jama’a, saboda suna zama a wuraren kazanta, shi yasa mafi yawan cutarwar da Aljannu ke yi wa dan Adam su ne ke yi!! (Allah ya tsare mu).

DALILIN DA YASA ALJANU KE SHAFAR DAN ADAM.

Yawancin Aljanu suna shafar dan Adam ne ta daya daga cikin wadannan dalilai guda 4:-

  1. Saboda zalunci da muguntar Aljanin.

  2. Da sunan kauna ko son da Aljani ke yi wad an Adam, kamar Aljani ya so mace mutum, ko Aljana ta so namiji mutum.

A gaba za mu yi bayani akan wannan matsalar, kuma shi ake kira da Jinnul Ashik (Namijin Dare) ko Jinnul Ashika (Macen Dare) insha Allahu.

  1. Saboda cutarwar dad an Adam ya yi wa Aljanun, kamar ya zuba masa rowan zafi ko ya taka shi, sai ya zo daukar fansa.

  2. Ko Bokaye da matsafa su turo wa mutum Aljanin.

CUTARWAR DA ALJANI KE YI WA DAN ADAM.

Aljanu na cutar dad an Adam ta hanyoyi guda 2, kamar haka:-

  1. Ta hanyar shiga jikin dan Adam:- Shine Aljani ya shiga jikin dan Adam gaba daya ko wata gaba, kamar hannu, kafa, Baya, Kirji, Kai, Ido ko Kunne, sai yayi ta cutar da marar lafiya yana wahalar das hi.

Wannan ya tabbata a cikin Hadisi, Manzon Allah (SAW) yace:

“LALLAI SHAIDAN (ALJANI) YANA GUDANA A JIKIN DAN ADAM AKAMAR YADDA JINI YAKE GUDANA”.

Ma’ana: Yana iya shiga duk inda jinni zai shiga, saboda bas hi da gangan jiki da zai hana shi hakan.

  1. Ta hanyar Shafar jikin dan Adam:- Shine ya sanya ciwo ko kuma ya lalata wata gaba daga cikin gabobin dan Adam, kamar ya lalata ko shanye hanu, ya sanya ciwo ko ya kurumtar da kunne, ko ya rike muryar mutum ko ya sanya wa mace ciwo a mara ko mahaifa, ko ya taba mata wata jijiya sai jinni ya yi ta zuba, da sauransu.

Irin wandannan Aljanun ba a samunsa a jikin marar lafiya, sai dai ayi ta amfani da magani wadda musulunci yayi umurnin amfani das hi, ta kuma hanyar mai kyau.

LOKOTAN DA ALJANI KE SHIGA JIKIN DAN ADAM.

  1. Yayin da mutum yake cikin matsanancin bacin raid a fushi.

  2. Yayin da mutum ya tsorita.

  3. Yayin da Mutum ya nitse cikin sabon Allah, kamar kallace-kallacen fina-finan banza na batsa.

  4. Yayin d mutum yaje cikin janaba, saboda babu garkuwa na tsarki a jikinsa.

ALAMOMIN SAMUWAR ALJANI A JIKIN DAN ADAM.

a. Yawan mantuwa mai tsanani.

b. Mutuwar wani bangare na jiki, hannu ko kafa wanda baya jin magani.

c. Yawan samun damuwa da kuncin rai.

d. Rashin nitsuwa a guri daya.

e. Yawan kokwanto.

f. Firgita a cikin barci.

g. Yawan mafarkin matattu.

h. Yawan mafarkin jinni ko ruwa.

i. Mafarkin maciji.

j.Jin motsi kamar ana binka a baya.

k. Cizon hakuri a cikin barci.

l. Yawan rashin bacci.

m. Yawan farkawa daga bacci.

n. Mafarkin Shanu.

o. Mafarkin saduwa ba bias ka’ida ba, kamar sau 3 fiye da haka a sati.

p. Yawan zubar jinin haila wanda ya wuce misali.

q. Yawan zancen zuci.

r. Rashin amincewa da mutane.

s. Yawan faduwar gaba.

t. Tafiya ko tsayuwa a cikin bacci.

u. Yawan mafarkin abubuwan ban tsoro.

v. Yawan yawace yawace ba bias qa;ida ba.

w. Yawan jin tsoro haka kurum.

x. Yawan jituwa tsakanin miji da mata.

y. Jin sauti kamar ana kiranka.

z. Dadewa a bandaki ba tare da wani dalili ba.

aa. Zancen zuci a bandaki.

bb. Mafarkin kyanwa (mage). Da sauransu.

Da zaran dan Adam ya ji wannan alamomin a jikinsa, to akwai alamar samuwar aljani a tattare

das hi, sai ya fara addu’a da yawan azkar, da yawaita karatun alku’ani.

Idan kuma ya fara jin ciwon kai, ciwon kirji, ciwon baya, ko ciwon gabobi, bayan wadncan alamomi da suke sama, sai ya ci gaba da addu’a tare da shan magani, in kuma abun yayi tsanani, sai ya nemi Malamim Ruqiyya (Ahlus Sunnah), su yi masa, karatun Alkurani. Allah ya tsare mu.

ABINDA AKE KIRA JINNUL ASHIK:-

Shi ne mace ta wayi gari tana yawan mafarki wani na saduwa da ita cikin barci, wannan al’amarin ya kasance ya yi yawa a tsakanin mata kuma har ya kai ga wasu cututtuka suna faruwa ga mace ko namiji ko kuma cututtukan da ba sa jin magani a yi ta wahala har a gaji.

DALILIN SAMUWAR JINNUL ASHIK:-

Malaman duniya sun bayar da fatawowi cikin Alqur’ani da Sunnah, kamar cikin Majmu’ul fatawa na Shaikul Islam ibnu Taimiyyah da littafin Ash-shifa’u bil qur’an minal jinnu wash shayadini na Ridha Ash-sharkawi da littafin Minhajul qur’an li’ilaj as-hir wal massi as-shaidani suka ce:

Wannan Aljani da ake kira jinnul Ashik yakan samu mace ta hanyoyi hudu kamar haka:-
Wata shi yake kawo kansa saboda rashin kyautata sutura da shigar banza na kayan zamani, wanda musulunci ya hana.
.
Wata kuma ita take kai kanta inda aljanun suke, kamar zuwa wajen bokaye.
Wata kuma sihiri aka yi mata saboda ta hada nema da wani maras tsoron Allah.
Wata kuma tana kyautata sutura, tana bin Allah, amma Allah zai jarrabe ta da wannan

shaidani.

A takaice dai wadannan hanyoyin da shi wannan shaidani zai zo wajen ta sai ya mayar da abin ya koma zuwa soyayya ya raba ta da kowa ya hanata yin aure ko ya rabata da mijinta ko ya hanata zaman lafiya da shi, shi kuma Aljanin ya ci gaba da zama da ita yana saduwa da ita ya dauke ta kamar matarsa kuma ya hana mijinta komai da ita, ya sa gaba da kiyayya a tsakani. Allah ya kiyaye.

HANYOYIN DA YAKE BI YA ZO MATA A MATSAYIN MIJIN DARE.

SUNE KAMAR HAKA:-
Yakan zo wa mace cikin barci ya dinga saduwa da ita cikin mafarki, ta fuskar mijinta ko wani wadda take jin kunya ko wadda bata sani ba ko dan uwanta ko ta siffar mace ‘yar uwarta.
Yakan zo mata a siffar mijinta yana saduwa da ita a zahiri ba a mafarki ba, amma kuma shaidani ne ba mijinta ba ne.
Yakan zo wa mace tana kwance ta ji kamar ana saduwa da ita, ita ba mafarki ba, ita kuma ba idon ta biyu ba.
Wata macen ta kan kwanta ta yi barci ba wadda ya sadu da ita, amma idan ta farka ta wayi gari sai ta ga kamar wani ya sadu da ita.

ALAMOMIN MIJIN DARE:-

Daga cikin alamomin da mace zata gane tana da wannan matsalar shine:-

Shi wannan shaidanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita cikin barci, yawanci mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayin, amma sai su dauka shirmen mafarki ne kawai, to a gaskiya ba haka bane. Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin za ka same ta tana fama da wadannan matsalolin, ko da za ka tambaye ta wadannan matsalolin za tace maka tana fama da su.

Daga ciki akwai:-
Bacin rai ba a mata komai ba, ta ji tana jin haushin kowa har ma da mijinta ko kuma ta ji kamar mijin ya sake ta, ta gaji da auren, da za ka tambayeta laifin mijin ba zata fadi laifinsa ba, wata rana ma ta ji tana tsanar ‘yan’yanta.
Yawan ciwon kai daga lokaci zuwa lokaci kuma baya jin magani.
Tsananin ciwon kirji da ciwon baya.
Tsananin ciwon mara lokacin al’ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin mace, shi ba al’ada ba ne, kuma ya kasu kashi 2; mai yauki da maras yauki ko mai kauri kamar koko tare da yawan kaikayi ko fitowar kuraje.
Ga yawan zubar ciki ko bari, ko kuma rashin samun ciki, amma za ta iya kasancewa ta dauki alamomi na masu ciki har ma ana zaton tana da ciki, amma ana kwana 2 sai ta canza kamar ba ciki ba, ko ta rinka yawan mafarki ta haihu.
Idan mijinta yana saduwa da ita tana jin zafi, ko kuma yana saduwa da ita ba zafi, amma bata samun biyan bukata.
Daf da magariba ta dinga jin zazzabi ko faduwar gaba ko yawan tsorata, ko kasala da bacin rai.
Idan ta dauki Alku’ani za ta karanta sai ta dinga jin kasala da hamma da hawaye da barci da zarar ta ajiye kur’anin sai ta ji wartsake kamar ba ita take jin barci ba.
Sannan kuma ko ta kwanta tana son yin barci sai ta kasa, ta yi ta juyi ta kasa barci, mijinta na zuwa kusa da ita sai ta dinga samun firgita da tsoro.
Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga kadewa ko ya yi ja, bakinta ya dinga bushewa ko yayi ja.
Yawan kaikayin ido da kaikayin kai na amosani, amma ba amosani ba ne.
Yawan kaikayin kunne da yawan kaikayin hanci kamar mura, amma ba mura bane, ko yawan kunburin ciki.
Yawan zuban jini daba na al’ada ba, ko jini ya rika yi mata wasa.

Sannan kuma har ma wacce bata da aure budurwa ko bazawara za ta iya samun wannan matsalar, amma ita bambancin da ke tsakanida ita wacce take da aure shine kamar haka:-

Ita marar aure za ta kasance duk lokacin da wani ya zo wajen ta da maganar aure kamar za a yi sai abin ya lalace daga wajen ta ko daga wajensa.

Za ta dinga samun munanan mafarkai tare da ganin wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita cikin barci ta fuskar da ta sani ko bakuwar fuska ko mace ‘yar uwarta.

Kuma za ta dinga yawan samun cututtuka masu wuyar magani har ma da yawan zubar da jini ko ciwon mara lokacin al’ada ko kasala lokacin karatun kur’ani, tana farawa sai hamma da kasala ya kama ta ko kuma idan ana sallama da ita, sai ta rinka jin faduwar gaba ko tsoro.

Kuma za ta rinka yawan samun sabani da kiyayya tsakaninta da iyayenta ko ‘yan uwanta ko jama’a ko kuma ta zama mai rashin kunya da rashin magana ga iyaye da sauran dangi.

Allah ya kiyaye.

GAME DA NAMIJI:

Dukkan wadannan bayanai da aka yi game da ‘yan uwa mata, to sukan iya samun da namiji, amma bambanci shine:-

Shi namiji macen Aljana ce za ta dinga zuwa wajensa ta zama ta raba shi da kowa sai ita kadai, ta dauke shi kamar mijinta, idan mai mata ne ta cire soyayya da sha’awa tsakaninsa da matarsa, kuma ta hana shi komai na ci gaban rayuwa ta mayar da shi marar kishin kansa da rayuwarsa.

Idan saurayi ne takan hana shi karatu ko ya fara ba zai gane ba, ko kuma inya gane ta hana shi karatun ko ta dinga sa masa wasuwasi da kokwanto lokacin jarrabawa ya fadi ko a kore shi a makarantar, in ya kama neman aure ko a ki shi ko shi ya ki, in ya kama sana’a sai ya yi ta samun matsala, kuma shi ba shan Giya, ko mata yake nema ba, kuma tasa gaba da rashin yarda tsakaninsa da iyayensa ko jama’a.

MAFITA:

Duk wadannan abubuwa da aka fada ba abubuwa ne sabbi ko baki ba, ba kuma yau ko jiya aka fara samun wannan matsalar ba, wannan matsalar an same ta tin zamanin Annabi (SAW) game da Aljani ko Aljana ya shiga jikin dan Adam namiji ko mace.

Imam Bukhari ya ruwaito hadisi zamanin Annabi (SAW) an samu wata mace ta zogaban Annabi da matsalar cutar Aljani ya kayar da ita, ta fadi, ta ce Annabi ya yi mata magani.

Sai Annabi (SAW) y ace mata, da a bar barki dad a cutar ki mutu ki shiga aljannah, da a yi miki addu’a ki warki, wane ki ka fi so?! Ta cewa Annabi (SAW) idan wannan cutar za ta zama sanadin shigata Aljannah, a barta da shi, amma ayi mata addu’a idan ya kada ita, ta dai na tsiraici.

Don haka wannan al’amari ba bako bane ga musulmi Ahlus Sunnah.

Komawa zuwa ga Allah (SWA) da kuma rike addu’o’in dad a Manzon Allah (SAW) ya ba muna safe, yamma da na shiga ban daki da fita, da na lokacin kwanciya, da na sanya sutura da cirewa, da na cin abinci, duk wadannan suna cikin littafin (HISNUL MUSLIM), sannan kuma sai wadannan hanyoyin da Malami suka bayar guda 11, ga me da mace ko namijin da suka samu kansu da namijin dare ko macen dare:

  1. Su kiyaye dokan Allah (SWA) da nisantar laifuka manya da kanana.

  2. Yawaita karatun Kur’ani a kawane hali a kuma kowane lokaci.

  3. Kyautata sutura (mace) hijabi, tin daga sama har kasa, mai kauri kuma mai fadi bana adoba.

  4. kiyaye cin halal wanda za a ci ko wanda za a nema.

  5. Yin sallah akan lokaci tare da kiyaye ilmin sallah din tin daga Annabi (SAW).

  6. Yawan yin Alwala lokacin da za a kwanta bacci da kowane lokaci.

  7. Yawan karanta Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasulu, kulhuwa, Falaqi da Nasi lokacin kwanciya.

  8. Yawan karanta Suratul Baqara a gida ko dakin da ake kwana da cire hoto ko na waye.

  9. Yawan Karanta:- LA’ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA

HUWA ALA KULLI SHAI’IN QADIR. Sau 100 da safe da yamma.

  1. Karanta BISMILLAHIL LAZI LA YADHURRU MA’A ISMIHI SHAI’UN FIL ARDHI WA LA FIS SAMA’I, WA HUWAS SAMI’UL ALIM. Sau 3 da safe da yammaa.

  2. Da Karanta: A’UZU BIKALIMATILLAHIT TAMMATI MIN SHARRI MA KHALAK. Sau 3 safe da yamma.

HANYA TA BIYU.

Game da wadanda suka tsinci kansu cikin wannan matsalar, ta jinnul Ashik, za ta samu tsabar habbatus Sauda, sai ta karanta Suratul Baqara gaba daya a cikin wannan tsabar, sai a dinga hayaki a dakin da take kwana, kuma sai ta tsuguna kan hayakin ya dinga shiga jikinta, za ta rinka yin haka da safe da lokacin da lokacin kwanciya.

Sai kuma amfani da magungunan Islama wadda musulunci ya karantar ayi amfani das u.

Wannan ba zan zayyana su a nan ba, saboda wasu dalilai.

Alhamdulillahi Ala kulli Haal!!!

Za a iya nemana ta wannan hanyar:

(mukhair1434@gmail.com) ko (mukhair2013@yahoo.com) ko ta wayar hannu Kira kawai (+962777854761), wannan kuma text kawai (+2348067676223). Ko ta wannan kafar da nake taskance rubutuna akai.

SANIN ILIMIN AURE KAFIN YINSA.

Godiya ta tabbata ga Allah (SWA) wanda ya halicci dukkan komai. Babu wani abu mai faruwa, sai tare da nufinsa da ikonsa da kaddarawarsa. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa, har ya zuwa ranar tashin Alkiyama.

Lokaci ya yi da da’awar Islama takai mu gane cewar komai na shari’ah baya halatta sai da iliminsa.

Don haka bai halatta ga wani ya yi nufin aure ba, har sai ya san hukuncin auren.

Amma za ka yi mamakin mai imani da Allah da Manzonsa komai nasa ya zama kara zube, babu sanin hukuncin Islama, ba shi da ilimin sauke farillan kansa, to gaya mun ya ya zai dora wa kansa hakkin waninsa, alhali sallah ma bawa bai karanta ba, wai kuma wannan shine za a ba shi tarbiyyar wata!

Ga shi ya yi aure wai zai yi rayuwar koyi da Manzon Allah (SAW). Kowa na kokari wajen neman ilimin rayuwar duniya, amma sha’anin rayuwar da ta hada da Allah ana yine da ka, ta ya ya wannan idan ya yi aure zai zama jagora kan hanyar Manzon Allah?!.

Don haka wajibine ga matasa kafin kowa ya doshi yin aure sai ya je ya karanta hukuncin aure da dukkan ilimin da ya shafi auren a cikin addinin musulunci, domin baya halatta ka aikata aiki sai kasan hukuncin addini a kansa, ashe a karkashin haka muke iya fahimtar cewar da yawa daga cikin masu kokarin aure daga samari baya halatta su yi aure a haka.

Ya zo cikin sharhin Ibn Majah “Abubuwa da yawa ba wajibi ne mutum ya yi iliminsu ba, amma ba ya halatta kuma ka aikata abin, idan ka tashi sai ka yi iliminsa”.

Misali: Ba wajibi bane kowa yasan ilimin kasuwanci, amma baya halatta ga musulmi ya fara kasuwanci sai ya yi iliminsa, haka ma aure iliminsa ba ya zama wajibi akan kowa, amma duk wanda ya yi nufin aure, baya halatta ya yi sai yasan hukuncinsa a cikin musulunci, kamar sanin ilimin aure, hakkin miji da mata, nauyin ilimi da rayuwar matansa da ibadarsu da sauransu.

To mai za ka ce ga wanda ya yi aure bai iya ko da Ahlari ba?!

Ga shi tinda ya yi wayo yake kokarinsa wajen karatun boko don neman duniya.

Don haka ‘yan uwa na nu yi kokari wajen neman yadda za mu sauke nauyin da ke kanmu.

Allah ya mana dace gaba daya amen.

ADON JIKI GA MATA

GABATARWA.
A wannan zamani da aka samu ci gaba a hanyoyin sadarwa, an wayi gari mata har ma da maza, suna kwaikwayon abinda suke gani na ado a gurin Kafirai, ba tare da sanin cewar yin hakan ya dace da shari’ar Musulunci ba, ko ya sabawa shari’ar. Wannan ya sanya ya zamo wajibi a bayyana wa mata haddin da shari’a ta ajiye musu, domin hana su kutsawa Zunubi ba tare da saninsu ba.
Kuma bayyana musu wadannan hukunce – hukuncen zai sanya su fahimci cewar musulunci ba hanyar rayuwa ce ta takurawa da ci baya ba, sai dai hanya ce ta maslaha, don haka musulunci ya sanya wa mata haddi na yin ado da kawata jiki, wanda zai zamo maslaha a gareta, mijinta da kuma al’umma baki daya. Muna godewa Allah da ya shiryar da mu da ni’imarsa akan hanyar Musulunci.
HUKUNCI NA FARKO.
Ana bukatar mace ta aikata abubuwan da suke sune halaye na cikar mutuntaka, wadanda suka kebantu da ita, kuma suka shafe ta.
Daga cikinsu a kwai yanke farce da gyara su, domin yanke farce sunna ce kamar yadda malamai suka yi ijma’i, kuma yanke farce tsafta ce, barin sa ya yi tsawo, ba a yanke ba, wannan abin muni ne kuma koyi da dabbobi ne.
Sa’anna farce yana boye datti, ya kuma hana ruwa saduwa da wani bangare na dan yatsa yayin alwala ko wanka.
Kuma sunna ne mace ta kawar da gashin hamata da na mara, domin yin aiki da hadisin da ya zo ingantacce akan haka.
Abin da ya fi shine ta yanke duk bayan sati ko kuma kada ya wuce kwana 40 ba ta yanke ba.
HUKUNCI NA BIYU. Abin da ake bukatar ta yi da gashin kanta, da gashin ido, da hukuncin yin lalle da tura gashi da shamfo.
¤ Ana bukatar mace ta raya gashin kanta, kuma haramun ne a gareta ta aske gashin sai dai in akwai larura. A Hadisin da Nasa’i da Bazzar suka ruwaito, Manzon Allah (SAW) ya nuna haramun ne.
Amma idan ta dan yanke ko ta rage gashin, domin ta kasa bashi kulawar da ya kamata saboda yawansa, to babu laifi a gurin wasu Malamai. Zan ci gaba.
Domin wasu daga cikin matan Manzon Allah (SAW) sun aikata haka bayan mutuwar sa, saboda an hana su yin aure bayansa, don haka bas u da bukatar yin ado dag a shi.
Amma idan ta rage gashin domin koyi da kafirai da fasikai, ko kuma don ta kamuntu da maza, wannan haramun ne ba tare da shakka ba, domin an hana mata su yi koyi da kafirai, haka kuma an hana su, su kamantu da maza, idan kuma ta yi haka domin ado shi ma bai halatta ba. Don haka musulunci yana bukatar mace ta kiyaye gashin ta, ta kuma kula das hi, kuma an hana ta tara gashin kanta a saman ta yayi tozo, ko kuma ta tara shi a keyarta, domin kamar yadda Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya y ace hakan ko yi ne da matankafirai.Imamu Muslim ya ya ruwaito hadisi, Manzon Allah (SAW) yana cewa “AKWAI WASU MATA DA ZA SU ZO KARSHEN ZAMANI, ZA A GANSU SUN SANYA TUFAFI, AMMA DUK DA HAKA TSIRANCIN SU A FILI YAKE, KUMA SUNA TAFIYA SNA KARAI-RAYA, KUMA ZA KA GA KAYUWAN SU KAMAR TOZON RAKUMI, Manzon Allah (SAW) yace “BA ZA SU SHIGA ALJANNA BA, KUMA BA ZA SU JI KO KANSHIN TA BA”.
Kuma kamar yadda aka hana mace ta aske gashin kanta, ko ta rage shi ba tare da dalili ba, haka ma an hana hada shi, ko ta kara shi da wani gashin.
A hadisin da Imamul Bukhari ya ruwaito, Manzon Allah (SAW) ya la’anci mata masu kara gashi da wadanda ake karawa.
Domin yin haka karya ce da yaudara.
(2). Ya haramta ga mace ta gusar da gashin idon ta ko na girarta, ko ta kawar da bangaren sat a kowace hanya, ta hanyar askewa ko yanke wa, ka ayi amfani da shaving powder, wannan duk haramun ne; domin Manzon Allah (SAW) ya la’anci mata ma su aikata haka da wadanda ake yi wa, haka kuma yin hakan canza halittar Allah ne, wanda Shaidan da ya yi shelan kuma yai alkawarin zai halarkar da ‘ya’yan Annabi Adamu ta hanyar ta, kamar yadda Alla (SWA) yak e gaya mana a cikin Suratul Nisa’I aya ta 119.
Haka nan yin shanfo ta hanyar kona gashi ko kuma amfani da sinadari, shima zai shiga layin wannan haramcin, domin shima wani nau’I ne na canza halittar Allah kuma koyi ne da kafirai.
(3). Haramun ne ga mace ko namiji, su cire hakori ko kuma a kankare tsakanin hakori da hakori domin abar fika, don nufin yin ado.Sai dai idan za a yi haka ne domin kawar da wani cuta (kamar a samu wani hakori ya fita daga layin jerin hakora) ko kuma saboda hakorin bashi da lafiya, to babu laifi, domin wannan zai shiga bangaren yin magani da kuma kawar da muni, sai dai ya kamata in mace zata yi haka ta samu likita kwararriya mace ko kuma namiji amintacce.
(4). Haramun ne mace ta yi zane a jikin ta, wanda ake sanya wani karfe a wuta sannan a yi zane da shi a jikin mace, sannan sai a sanya kwalli ko tawada a gurbin.Manzon Allah (SAW) ya la’anci wacce ta ke yi da wadda aka yi wa a jikinta.
(5). Hukuncin Kunshi (Lalle) da rinin Gashi.
a. Kunshi:
Imam Nawawy ya fada a cikin littafinsa ALMAJMUU cewa: Amma yin kunshi a hannu da kafafu da lalle, mustahabbi ne ga matan aure, saboda hadisai mashuhurai da suka zo a kan haka.Kuma bai dace mace ta sanya janfaece a yatsunta ba, saboda zai hana mata tsarkin alwala da wanka.
b. Rini:
Idan mace tana da furfura a gashin kanta, za ta iya rinawa, amma kada ta rina shi dab akin launi, domin Manzon Allah (SAW) ya hana wannan, sai dai ta rina shi da wani launi, kamar ta rina shi da lalle.Amma bai halatta mace ta rina gashin kanta wanda yake baki zuwa wata kalar ba, domin shi baki shine aka sani wajen kyau ga mace, kuma babu wani dalili da zai sat a canza shi zuwa wata kalar, domin shanza shi zuwa wata kalar koyi ne da kafirai.
HUKUNCIN NA UKU.
Siffar Tufafin ‘ya mace musulma:
1. Wajibi ne tufafin ‘ya mace musulma, ta zama isash-shiya, wacce za ta suturce dukkan jikinta daga maza wadanda ba muharramanta ba, kuma ba za ta bude jikinta ga muharramanta tab a, sai dai abinda al’adan ce ake budewa, kamar fuska da tafukan hannnaye.
2. Wajibi ne ya zamanto zai suturce jikinta ta yadda ba za a iya hango launin jikin tab a.
3. Wajibi ne kada tufafin mace musulma ya zamo matsatstse, ya na fito da surar jikinta, kamar dinkin da mata suke cewa (SEE MY SHAPE) ko (SHOW MY BACK), da sauransu.
Manzon Allah (SAW) ya ba mu labarin matan karshen zamani, wadanda suke sanya tufafi da baya rufe tsiraricin su, saboda rashin kaurin sa, ko ya matse jikin su, ko kuma bai isa ya rufe tsiraicin sub a, Manzon Allah (SAW) y ace; irin wadannan mata ba za su shiga aljanna ba, kai ba ma za su ji kanshin taba. Allah ya kiyaye mu.
4. Ba a son tufafin mace musulma ya zama wanda zai kamanta tad a maza, domin Manzon Allah (SAW) ya la’anci maza masu sanya kaya irin ta mata, da mata masu sanya kaya irin ta maza.Kuma idan mace ta saka za a ga tayi kama da maza, domin yawancin kayan da maza suke sakawa, idan mace ta sanya su, ba za su rufe al’auranta kamar yadda shari’a take so ba. Don haka ko da mace za ta sanya wando, ana bukatar ya zama mai fadi, kuma ta dora doguwar riga akai, wacce za ta rufe har kwaurinta.
5. Kada tufafin mace ya zamanto mai daukan ido ne saboda launin sa ko zanen sa. Idan mata suka sanya irin wannan tufafin domin zuwa biki ko unguwa, wajibi ne su rufe shi da wani zanen ko hijabin su.
FADAKARWA;
1. ba lallai bane ace tufafin da mace za ta sanya ya zama baki ba, sai dai abinda ba a so shine ta sanya abinda zai ja hankalin maza a waje, domin hakan fitina ne a gar eta da kuma maza.
2. Wajibi ne mata su san cewa wuyan su da kwaurin su da kafafun su duk al’aura ce, don haka wajibi ne tufafin su ya zamanto wanda zai rufe su.
Wassalamu Alaikhum.
Muhammad Albani Misau.
2/05/2015

KUKAN KURCIYA……….

-Duk da yawan ruwan da’di da yake saukowa daga sama zuwa cikin teku, amma baya iya canja ruwan tekun nan daga na zartsi
zuwa na da’di….

Dan haka kar ka wahalar da kanka domin wasu, duk irin qoqarin da zaka yi akan su ba zaka iya canja su ba.

  • A koda yaushe mai hassada a gareka na maka kallon mai girman kai… yayinda masoyinka ke maka kallon mutumin kirki, kada ta farkon ta dameka kada kuma ta biyun ta ru’deka….

  • Kada kaji zafi yayin da wani ya musanta alkhairanka a gareshi, domin wutacen titi ma ana mancewa da su yayinda hasken rana ya bayyana!!!

  • Bishiya ta fa’di sai da kowa yaji sautin fa’duwarta, a yayinda daji guda yayi kore shar da yabanya ba tare da an ji sauti ko ka’dan
    ba… mutane basa damuwa da ayyukan nasararka kamar yadda suke damuwa da akasin hakan…. kai dai kayi domin Allah kawai.

  • Wasu mutanen kamar littafi mai kyau da tsada suke, bangonshi babu qyaleqyale balle ya ‘dauki hankali amma cikinshi fal yake da abubuwa masu amfani…. yayinda wasu ke ‘dauke da bango mai ‘daukar hankali amma fa ba sa qunshe da wani abu na amfanin azo
    a gani…. kada ka bari qyalqyalin bango ya ru’deka akan haqiqar abinda littafin ya qunsa!!!

MUHAMMAD ALBANI MISAU.

4/9/2015.

TAKAITACCEN BAYANI DANGANE DA HASSADA DA YADDA ZA A MAGANCETA A TSAKANIN AL’UMMA. 1

GABATARWA.
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam da Alayensa da Sahabbansa gaba daya da wadanda suka biyo bayan su da kyautatawa.

Wannan wani takaitaccen bayani ne akan abinda ya shafi HASSADA da yadda za a magance ta a tsakanin al’umma, nayi nazarin rubuta wannan takarda ne bisa matsaloli da suke shiga tsakanin al’umma a yanzu ta dalilin hassada, musamman daliban ilimi, da kuma masu hali, kai dama dukkan al’umma gaba daya, wannan yasa na ga ya kamata na yi rubutu don jawo hankalin ‘yan uwa na akan illar da Hassada take haifarwa da hanyar da za a magance ta a tsakanin al’umma gaba daya.

Allah na ke roka yasa wannan takarda ta zama hanya da sanadin magance wannan illar gaba daya ameen.
Fakiri mai neman gafara da kuma yardar Ubangijinsa.

MUHAMMAD MUHAMMADALBANI MISAU.

 

 

 

(1). Ma’anar HASSADA:

Itace mutum ya yi burin gushewar wata ni’ima daga mai ita, ko dai ni’imar ta addini ko wani abun duniya.

 

(2). KARKASUWAR HASSADA:-

Mutane ta bangaren Hassada sun ka su zuwa gida biyu.

a. Akwai wanda yake burin ni’imar dan uwan shi ya gushe, kuma ya dobe shi da Ido (Kambun baka) sai ya cutar da shi saboda Hassada.

Kambun baka gaskiya ne yana kai mutum zuwa ga kabari.

b. Akwai wanda yake hassada wa mutane, yana son ni’imar wanda yake wa hassadar ya kau (ya talauce) ko ni’imar ta dawo wajen sa, ko dukkan su su
ta shi a tutar babu.

 

(3) HASSADA TAKAN SA MAI YINTA YA WUCE IYAKA DA ZALUNCI:-

Hassada takan sanya mai yinta ya wuce iyaka, har ta kai shi ga zalunci, da dukkan wasu abubuwa, har ta kai shi ga yin kisa.

Misali:-

a. Hassada ita ta sanya Qabila ya ka she ‘dan uwan sa Habila.

Allah Subhanahu wata Ala yana ba mu labari ya ce:-

“KUMA KA KARANTA MUSU LABARIN ‘YA’YAN ANNABI ADAMU DA GASKIYA. A LOKACIN DA DA SUKA BAYAR DA BAIKO, SAI AKA KARBA DAGA DAYAN SU BA A KARBA DAGA DAYAN SU BA”

Allah ya karba daga habila bai karba daga Qabila ba, sai Qabila ya ce, (Saboda Hassada wa ‘dan uwan sa): “LALLAI NE ZAN KA SHE KA.”
Sai Habila ya ba shi amsa da cewa:
“ABIN SANI DAI, ALLAH YANA KARBA NE DAGA MASU TAQAWA. LALLAI IDAN KA SHIMFIDA HANNUNKA ZUWA GARE NI DOMIN KA KASHE NI, (ni) BAZAN ZAMA MAI SHIMFIDA HANNUNA ZUWA GARE KA BA, DOMIN IN KASHE KA, LALLAI NI, INA TSORN ALLA UBANGIJIN TALIKAI”. [Suratul Ma’idah aya ta 27-31).

b. Yusuf ‘yan uwan sa sun yi ikirarin su kashe shi, sai suka hadu akan suna ma su cewa:
“KU KA SHE YUSUFU, KO KU JEFA SHI A WATA KASA, FUSKAR UBAN KU TA WOFINTA SABODA KU, SAI KUMA KU KASANCE A BAYANSA MUTANE SALIHAI” [Suratu Yusuf aya ta 1-10].

Dalilin daya kawo haka shine Hassada, sai suka dauke shi suka jefa shi a Rijiya don ya mutu.
Wannan sakamakon Hassada kenan.

(4) HASSADA DABI’UN SHAIDANUN ALJANU DA MUTANE:-

Ka yi duba zuwa ga Iblis, Ya ga Annabi Adamu a cikin Aljannah kuma Allah ya halicce shi da hannunsa ya kuma busa masa rai, Mala’iku kuma suka masa sujjada. Sai Iblis (Shaidan) ya yi wa Annabi Adamu Hassada don ya fitar da shi daga Aljannah, Iblis ya bi hanyaoyin da zai bi har ya ci nasara, sai Annabi Adam ya fito daga aljannah, saboda wata hikima da Allah ya ke so.
Kaiton Iblis da ya kai wannan makurar har shela ya yi na ya ki da da Annabi adamu da zuriyar sa har ya zuwa ranar tashin Alkiyama.
Allah SWA ya ce:
“(Iblis yace) INA RANTSUWA DA HALAKARWAR DA KAYI MINI, ZAN KAWAR DA SU HANYARKA MADAIDAICI” [Suratul A’araf Aya ta 16].

 

(5). HASSADA TANA DAGA CIKIN ADON YAHUDAWA:-
Za mu ci gaba insha Allahu.

ZAKKAR FIDDA-KAI DA YADDA TAKE A MUSULUNCI

Idan Azumi ya kai dab da karshe, akwai Zakkar abinci da ake bayarwa don dada samun lada a wurin Allah da kuma kankare zunubban da suka yi saura na miyagun maganganu da makamantansu, shi ya sa ma ake kiranta da sunan “ZAKKAR FIDDA-KAI”.
HUKUNCIN ZAKKAR FIDDA-KAI:

Bayar da wannan Zakkar wajibi (farilla) ne, kamar yadda Hadisin Abdullahi Dan Umar ya nuna. [Riwayar Bukhari da Muslim].
Kuma ta na wajaba ne a kan ‘da, ko bawa namiji ko mace, babba ko yaro, matukar dai musulmi ne wanda ya mallaki abincin wuni daya, na sa da na iyalansa, ba sai wanda ya mallaki dukiya mai yawa ba.

Abdullahi Dan Abbas yace: “MANZON ALLAH SAW YA FARLANTA ZAKKAR FIDDA KAI, TSARKAKEWA NE GA MAI AZUMI, DAGA MAGANGANUN DA BA SU DACE BA, KUMA ABINCI NE GA MISKINAI..” [Riwayar Abu Dauda, Ibnu Majah ds].
Abdullahi Dan Umar kuma cewa ya yi: “MANZON ALLAH SAW YA YI UMURNI DA ZAKKAN FIDDA KAI GA YARO DA BABBA, ‘DA DA BAWA, DAGA WADANDA KUKE KULAWA DA SU” [Riwayar Daru Kudniy].

Don haka mai gida mai hali zai ba da nasa da na iyalansa da kuma yaransa gaba daya wadanda dai suke karkashinsa, Sun yi azumi ne ko ba su yi ba, don faranta ran talakawa da miskinai ranar sallah kada su je bara ko roko, ana cikin farin ciki su kuma suna bakin ciki, shi ya sa aka ce a ba su don a faranta mu su rai.

ABINDA ZA A BAYAR:

Za a bayar da Sa’i guda ne na kowani mutum daga dukkan nau’in abin da ake kiransa abinci, ba lallai sai dabino ko Sha’ir ko Alkama ba, wannan shi ne bayanin da malamai suka tabbatar, cikinsu kuwa har da Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah .
Don haka za a iya bayar da sa’in dawa, gero, masara, shinkafa da garin hatsi, ko na kwaki, matukar dai abinci ne babu laifi.

[Dun karin bayani duba Sifatu Saumin Nabiyyi SAW].

A kwai Malaman da suke ganin in har akwai bukatar a bayar da kima, ko kudi, ana iya bayarwa, amma a bayar da abinda shi ya fi tun da dai tambarin talaka fa cikinsa ne!

KARIN BAYANI:

Sa’i shi ne Muddin Nabiyyi guda hudu, cikin tafukan hannun matsakaicin mutum a hade shi ne Muddin Nabiyyi.

LOKACIN FITARWA:-

Ana bayar da wannan Zakkar ne ana gobe sallah kafin a fita zuwa masallaci, kamar yadda Hadisin ‘Dan Umar ya nuna cewa “MANZON ALLAH SAW YA YI UMARNI DA BAYAR DA ZAKKAN FIDDA KAI KAFIN FITAN MUTANE ZUWA MASALLACI” [Bukhari da Muslim].

Amma ya halatta a bayar kwana daya ko biyu kafin sallah, saboda maganan Nafi’u da ya yi na cewa “ABDULLAHI ‘DAN UMAR YA KASANCE YANA BA DA WADANDA SUKE KARBAN (Zakkar), SUN KASANCE ANA BA SU NE KUWA KAFIN RANAR SALLAH DA KWANA ‘DAYA KO BIYU” (Bukhari da Muslim).

Don haka ni ina ganin bayarwa kafin kwana ‘daya ko biyu shi ya fi, don mutane su samu daman sarrafa abin da aka ba su, sai dai idan Zakkar da shinkafa ce ko gari, wannan kam ba ya bukatar wata wahala, ko ranar sallah ana iya bayarwa.

WANDA ZA A BA WA:-

Za a bawa miskini ne ko fakiri wanda ba ya da hali, kamar dai yadda Annabi SAW ya ambaci lafazin Miskini, to shi ne za a ba shi, ba lallai sai an rarraba ga wadanda aka ambace su a cikin Ayar Zakka ba cikin suratul Taubah, amma wani yana iya hawa tudu biyu, a ba shi don ya cancanta, sannan sai ya bayar don ya samu wadatuwa.
Kuma lallai ne a bayar da zakkar kafin a tafi masallacin Idi, don Annabi SAW ya ce: فمن أداها قبل الصلاة فهي زكاة مقبولة ومن أداها بعد الصلاة فهي صدقة من الصدقات”
“DUK WANDA YA BAYAR KAFIN A JE SALLAH, ZAKKA CE KARBABBIYA, WANDA YA BAYAR BAYAN SALLAH KUMA SADAQA CE DAGA CIKHN SADAKOKI KAWAI” [Riwayar Abu Dawud da Ibnu Majah].

Don haka sai a yi kokari a bayar da wuri don a kwantar wa miskinai da hankali, a sanya musu farin ciki da walwala, a kuma rufa mu su asirinsu, don su ji dadin shagulgulan Idi tare da iyalansu da abokansu da ‘yan uwansu.

 

Wannan shine dan takaitaccen bayani da zan yi akan ZAKKAR FIDDA KAI.
Allah ya mana dace ya kuma karbi ayyukammu amen.

Da fatan ba za ku manta da ambatun sunana a cikin addu’o’inku ba