RAYUWAR MUSULMI A YAU.

بسم الله الرحمن الرحيم

GABATARWA.

Wannan kalma tana iya daukan fiskoki, ko ma’anoni guda uku:-

(1) Rayuwar musulmi da ‘dan uwansa musulmi a kowani guri da kowa ce kasa.

(2) Rayuwar musulmi da wanda ba musulmi ba ta wajen zaman takewar yau da kullum.

(3) Rayuwar musulmi ga shi kansa wajen bin tsarin musulunci kamar yadda Allah ya tsara masa bisa karantarwar Manzon Allah SAW.

Wadannan fiskoki guda uku idan mukayi tadabburin ma’anonin ayoyin Alqur’ani mai girma za mu ga Allah SWA ya yi mana bayaninsu dalla dalla, daya bayan daya a cikin suratul An’ami Aya ta (151 – 153).

“قل تعالول أتل ما حرم ربكم عليكم, ألاَ تشركوا به شيئاً, وباالوالدان إحساناً ولا تقتلوا أولادكم من إملاق نحن نرزقكم و إياهم, ولا تقربوا الفواحش ماظهر منها وما بطن ولا تقتلوا النفس التى حرم الله إلا بالحق, ذالكم وصىكم به لعلكم تعقلون ” (151).
“ولا تقربوا مال اليتيم إلا بالتى هى أحسن حتى يبلغ أشده, وأوفواْ الكيل والميزان بالقسط, لا نكلف نفساً إلا وسعها, وإذا قلتم فاْعدلواْ ولو كان ذا قربى و وبعهد الله او فواْ, ذالكم وصىكم به, لعلكم تذكرون” (152).
“,أن هذا صراطى مستقيماً فاْتبعوه, ولا تتبعواْ السبل فتفرق بكم عن سبيله,ج ذالكم وصىكم به, لعلكم تتقون” (153).

Dai dai wadannan ayoyi Imam Ibn khathir cikin Tafsirinsa, ya hakaito maganan Abdullahi ‘dan mas’ud (RA) y ace

“WANDA YAKE SO YAGA WASIYYAR MANZON ALLAH (SAW) WACCE YA SANYA TAMBARINSA AKANTA, TO YA KARANTA WADANNAN AYOYI GUDA UKU”.

Sa’anan yana da kyau mu fahimci cewar bayana nufin akwai wasu ayoyi wanda Manzon Allah (SAW) ya kebe su ya musu tambari na musamman bai yu wa wassu ba, abin nufi anan shine wadannan ayoyi guda uku, hani da umaurni ko mas’aloli da Allah ya yi bayaninsu a ciki, Manzon Allah(SAW) ya karfafasu wa sahabbai akanta, kamar yadda Imamul Bagawi ya kawo cikin tafsirinsa. (Ma’alimut Tanzil, mujalladi na 2).

Sa’annan wadannan ayoyi guda uku akwai wasu mas’aloli guda goma (10) a cikin su, wadanda malamai suka musu suna da (WASAYAL ASHRA) ma’ana wasiyyoyi guda goma.

Kuma in muka fahimci kowace daya daga cikin wasiyyoyin nan guda goma (10), tana iya kasancewa cikin fiskokin rayuwar musulmi guda uku wadanda muka ambata su a baya.

Wadannan mas’aloli guda goma sune:

  • Kada kayi shirka wa Allah.

  • A kyautata wa iyaye.

  • Kada a kashe ‘ya’ya don tsoron talauci.

  • Kada a kusanci Alfasha a fili da boye.

  • Kada a kashe wata rai da Allah ya haramta sai da haqqi.

  • Kada a kusanci dukiyar maraya sai da kyautatawa.

  • A cika mudu da sikeli da adalci.

  • Abi hanyar Allah da Manzosa ba tare da yin bidi’a ba.

-In za a yi Magana a yi adalci
ko akan makusanci ne.

  • A cika Alkawarin da aka dauka wa Allah.

Wadannan sune mas’aloli guda goma wanda ayoyinnan guda uku suka kunsa, sa’annan idan muka dibi mas’aloli guda uku daga ciki:

*Kada a kashe ‘ya’ya don tsoron talauci.

  • Kada a kashe wata rai da Allah ya haramta sai da haqqi.
  • Kada a kusanci dikiyar maraya said a kyautatawa. –

Wadannan sun sha fi musulmi da ‘dan uwansa musulmi kai tsaye.

Sa’annan idan muka dubi mas’aloli guda uku daga ciki har wayau:

  • In za a ayi Magana a yi adalci ko akan makusanci ne.

*A kyautata wa iyaye.

*A cika mudu da sikeli da adalci.

Su kuma wadannan sun shafi tsakanin musulmi da wanda suke mu’amala das hi kai tsaye ko dab a musulmi ne ba.
Sa’annan sauran mas’aloli guda hudu:

  • Kada kayi shirka wa Allah-
    Kada a kusanci Alfasha a fili da boye.

-Abi hanyar Allah da Manzosa ba tare da yin bidi’a ba.
-A cika wa Allah Alqawarinsa.

Wadannan su kuma sun shafi shi musulmi ne akaran kansa.

Amma kuma wadannan mas’aloli guda goma da suka zo daga cikin wadannan ayoyi guda uku, wajibine akan dukkan musulmi ya kiyayesu kuma kada yayi sakaci das u, don hadisi ya zo daga Ubadatu dan Samit y ace Manzon Allah SAW yace: “WAYE CIKINKU ZAI YIMIN MUBAYA’A AKAN ABUUKU?” yace sai Manzon Allah SAW ya karanto wadannan ayoyi har zuwa karshensu, sai Manzon Allah ya ci gaba da cewa;

“DUK WANDA YA CIKASU TA LADANSA YANA GURIN ALLAH, DUK WANDA YA TAUYE WANI DAGA CIKINSU SAI ALLAH YA KAMASHI A DUNIYA, TO WANNAN AZABARSA, AMMA WANDA ALLAH YAJIN KIRTA MASA ZUWA LAHIRA, TO AL’AMARINSA YANA GURIN ALLAH IN YA SO YA MASA AZABA IN YA SO YA YAYEFA MASA” (duba Tafsir na Ibn Kathir, mujalladi na 2).

Imamu Hakim shi ya ruwaito wannan Hadisin a cikin littafinsa (ALMUSTADRAK), amma Imam Ibn Khathir ya hakaito shi a cikin tafsirinsa dai – dai fassarar wadannan ayoyi.

Sa’annan ina mai rokon Allah ya taimake mu wajen kiyaye hakkokin daya dora akan mu, tsakanin mu da shi da kuma na ‘yan uwan mu, musulmi da wanda ba musulmi ba, amen.

NAZARI A YAU.

‘Yan uawana musulmi kowa mai shaidane a cikinku akan halin da musulmai da musulinci ke ciki a yau, ta bangaren musulmin su kansu da kuma wadanda ma ba musulman ba, a duniya baki daya bawai a wata kasa ko a wani gari ba.

Musulmi yana cikin kaskanci da rashin mutunci da wulakanci, da zaman dar-dar, wasu alkawarin Allah ne da yayi akan wadanda suke dogewa da yin Imani na gaskiya, kamar yadda Allah SWA ya fada a cikin Alqur’ani mai girma:

“ولنبلونكم بشيء من الخوف والجوع ونقص من الأموال والأنقس والثمرات قل وبشر الصابرين” (155)
” الذين إذآ أصابتهم مصيبة قالواْ إنا لله و غنا إليه الراجيعون.(156).
” أوْلئك عليهم صلواتٌ من ربهم ورحمةصلى وألئك هم المفلحون.(157).

“WALLAHI ZAMU JARRABE KU DA WANI ABU DAGA TSORO DA YUNWA DA TAWAYA CIKIN DUKIYA DA RAYUKA DA ‘YA’YAN ITATUWA (Amfanin gona), AMMA KA YI ALBISHIR WA MASU HAKURI. SUNE IDAN WATA MUSIBA TA SHAFE SU SAI, SU CE LALLAI DAGA ALLAH MUKE KUMA GARE SHI ZA MU KOMA. WADANNAN SUNE SUKE DA SALATOTI DAGA MAHALICCINSU DA JINKAI KUMA WADANNAN SUNE SHIRYAYYU” (Baqara, Aya ta 155-157).

Kuma duk wanda ya shiga cikin tsanani saboda ya yi riko da addini to jimawa kadan zai samu sauki.

Allah SWA yana cewa
“LALLAI TARE DA TSANANI AKWAI SAUKI” (Sharhi, Aya ta 5).

Sa’annan kuma Allah zai bas hi mafita da fadinsa madaukaki

“DUK WANDA YA JI TSORON ALLAH, ALLA ZAI BA SHI MAFITA” (dalaq: 2).

To amma wadannan sune mafi kadanci a rayuwa da muke ciki a yau, don hadisi ya tabbata daga Abu Huraira (RA) yace, Manzon Allah SAW yace:

“ZAMANI YANA KUSANTOWA, AIKI ZAI YI KADAN ZA A RINKA YIN BAKAR ROWA KUMA FITINA ZA TA YI YAWA” (Bukhari 4/6652, muslim 1/157).

Da fadin Manzon Allah SWA har wa yau:

“WATA YANKI BAZATA GUSHEBA CIKIN AL’UMMATA TANA KAN GASKIYA, BA ZAI CUCESU BA, DUK WANDA YA SABA MUSU, HAR SAI AL’AMARIN ALLA Y NZO” (Muslim).

Amma mafiya yawan yawa cikinmu ba haka muke ba, mun sake tafarkin gaskiya, haramun ya zama halal, halal kuma ya zama haram, abu mummuna ammai das hi kyakkyawa, sabawa Allah ya za ma kamar da’a wa Allah, tarbiyyar musulunci ammai das hi tsohon yayi, Alqur’ani ya zama sai dai a yi takara an kaurace wa hukuncinsa, alhali babu wani alkhairi face yana cikin Alqu’ani.

Hadisi ya tabbata Manzon Allah SAW yace

“NA BAR WA SU ABUBUWA GUDA BIYU A CIKINKU, BA ZA KU TABA BACE WABA MATUKAR KUNYI RIKO DA SU, LITTAFIN ALLAH (Alqur”ani) DA SUNNATA”.

Musulmi ya sauke Alqur’ani yasa kae sunnar Manzon Allah SAW, in dai musulmi yayi haka wa kansa, mai yasa kaskanci ba zai same ba,tin da ya sake hanyar addininsa ta gaskiya.

Hadisi ya tabbata daga Abdullahi dan Umar RA yace, na ji Manzon Allah SAW yana cewa

“IDAN KU KA YI CINIKIN IINA KUKA RIKE JILAR SHA NU KUMA KU KA YARDA DA SHUKE-SHUKE, KUMA KUKA BAR JIHADI, TO ALLAH ZA SHINFIDA MUKU KASKANCI, BA ZAI CIRE SHIBA HAR SAI KUN KOMA ADDININKU” (Abu Dauda da Imam Ahmad).

Ma’anar (IINA), wani nau’I ne na saye da sayar wa, amma akwai riba a ciki, duk da cewar wasu daga cikin Malaman Fiqhu suna ganin babu laifi, amma mafi ingancin Magana wannan kasuwancin ta (IINA) bata halarta ba.(Mai neman Karin bayani ya duba Attarbiyatu wat tarbiyatu na Imam Albani).

Sa’annan wannan hadisin, kamar yadda Imamu Albani yace,” ma’anarsa idan kuka shagalta da tara kayan duniya da neman arziki, da tawilin cewa neman arzikin halalne, hart a kai mutum yana gab a abin day a zo nema duniya sai arziki kawai, to wannan shike sa mutum ya manta da Allah, kuma yayi ta saba masa”. Ya ci gaba da cewa “Wannan hadisin yana dga cikin alamomin Annabci na Manzon Allah SAW. Kamar yadda ‘yan uwa suke gani tabbas wannan kaskancin ya tabbata a cikin mu, kamar yadda Manzon Allah SAW ya fada”.
TARBIYYAR MUSULMI

Tabbas tarbiyyar musulunci iatce tarbiyya ta kololuwa, kuma babu tarbiyyar daya fishi da cewa da ‘dan Adam, kai har ma da duniya baki daya. Idan muka dubi lokacin jahiliyya mutum yakan sassake itace da hannunsa sa’annan ya mai das hi abin bautarsa, kuma gare shi yak e kai kukansa da neman agajinsa, wani kuma dutse yake dauka mai kyau ya maid a shi abin bauta.

Babu wautar daya shige irin wannan. Wani kuma sai yce duk dunuyya babu abinda ya fiso illa lokacin da dare yayi, yayi tatul da giya, yayi ta surkulle shi kadai, sa’annan ga zinace-zinace, su a gurinsu zina ba laifi ba ne, sai dai anyi a fili, amma idan an boye, babu laifi, ga fashi da makami, su a gunsu fashi da makami jarunta ne, duk wanda yafi karfi shine shugaba, sa’annan wani babban al’amari dab a komai bane a gunsu shine: kisan kai, hasalima ‘yan’yansu suke kashewa don tsoron talauci da abin kunya (wai a fadinsu), sai yake-yaken da babu gaira ba dalili, da fitan ballagaza da mata keyi, sa’annan auratayya rututu babu iyaka, su agunsu mutum zai iya auran mata sama da ‘dari ma ba laifi, sa’annan babu babba ba yaro.

Amma da Manzon Allah SAW ya kawo musu sakon Allah SWA, duk da cewa ya same su cikin lallacewa da gafala, kamar yadda Allah SWA ya fada a wata aya:

“DON KA YI GARGADI WA WASU MUTANE DA BA’A’TABA GARGADI WA IYAYENSU BA, SU SUNA CIKIN GAFALA” (Yasin Aya ta 6).

Amma duk da haka Manzon Allah (SAW) saboda iya karantarwarsa da kuma kykkyawar dabi’arsa, ya rika binsu sako-sako, wuri-wuri yana musu wa’azi da Alqur’ani, cikin yardar Allah, dabi’unsa ya canza, imaninsu ya karfafa, suka yi watsi da ‘dabi’un jahiliyya suka rike na musulunci har Allah yayi musu yabo a cikin Alqur’ani a wurare daban daban.

Kuma suka kasance cikin daukaka bayan sunyi fama da kaskanci, a lokacin jahiliyya, kamar yadda Sayyiduna Umar (RA) yake cewa:

“DA MUNA CIKIN KASKANCI, SAI ALLAH YA DAUKAKA MU DA ALQURANI, IDAN MUKA NEMI DAUKAKA BATA ALQUR’ANI BA, TO ALLAH ZAI KASKANTAR DA MU” (Duba Muqaddimatu fi Usulil tafsir).

Ma’ana: Wadancan dabi;un su suka jefa su cikin kaskanci da lalacewa, sa’annan Alqur’ani da bin tsarin musulunci shi ya fidda su daga cikin kaskanci ya sa su cikin ‘yanci da daukaka.
HALINMU A YAU.

Mu a halin da ake ciki ko a rayuwar mu ta yau, duk dabi’un jahiliyya babu daya wacce ba a yenta a yanzu ko kuma ince anzarce lokacin jahiliyyar farko, wannan kuwa shine ya afkar da mu cikin kaskancin da muke ciki a yau, Allah (SWA) yana cewa

“LALLAI ALLAH BA SHI CANZA WA MUTANE, SAI DAI SUNE SUKE CANZA WA KAWUNANSU” (Ra’adi, Ayata 11).

SHAWARWARIN GYARA.

(1). Wajibine ko wani dayan mu ya gyara alaqarsa da Mahaliccinsa Allah (SWA).

(2). Wajibine kowa ya gyara alaqarsa da jama’an da yake mu’amala das u.

(3). Wajibine kowa ya maid a hankali wajen tarbiyyar iyalansa bisa tsarin musulunci, don ya tsira a wajen Allah ranar da ‘ya’ya da dikiya ba za su amfanar das hi da komai ba, sai tsoron Allah.

(4). Wajibine kowa ya da mu da gyaruwar zuciyarsa, don samun karbuwar ayyukansa kamar yadda wani mai da’awar musulunci ke cewa

“KU TSAYAR DA DAULAR MUSULUNCI A ZUCIYARKU, SAI TA TSAYU CIKIN KASASHENKU”.

(5). Wajibine kowa ya maid a hankali wajen neman ilimin addini da rayuwa, ta yadda zai bautawa wa Allah cikin ilimi bad a jahilci ba.

Wannan shine abinda ya sauwaka daga gare ni, ina kuma rokon Allah ya ya taimake mu ya ba mu ikon aiki da abinda muka karanta, ya kuma tabbatar mana da daular musulunci a kasata Najeriya da duniya gaba daya amen.

Wa subhanakallahumma wabihamdika astagfiruka wa’atubu ilaikh.

MUHAMMAD MUHAMMAD ALBANI MISAU.